Wata sanarwa da babban sakataren na MDD ya fitar ta hannun kakakinsa, ta bayyana cewa, ya damu matuka da abubuwan da ya lura suna faruwa a yankin gabas ta tsakiya.
Don haka ya bukaci kasashen da ke yankin, da su kare aukuwar duk wani tashin hankali, su kuma yi kokarin warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, ta hanyar amfani da matakai na diflomasiya. Yana mai bayyana kudurinsa na goyon bayan irin wannan mataki a duk lokacin da bangarorin suka bukaci hakan.
Rahotanni na cewa, kasashen Saudiya da hadaddiyar daular Larabawa da Bahrai da Masar da Yemen da Maldives, duk sun yanke shawarar katse huldar diflomasiya da kasar ta Qatar ce, bisa zarginta da hada baki da kasar Iran wajen maraba kungiyoyin 'yan ta'adda baya.(Ibrahim)