James Zhan, darektan sashin zuba jari da kamfanoni na UNCTAD, ya ce yadda kasar Sin take kara zuba jari a kasashen waje ya nuna bukatar kamfanonin kasar ta kara taka rawa a kasuwannin duniya. Bisa yanayin da kasar ke ciki na kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da habakar hadin gwiwa tare da sauran kasashe ta fuskar masana'antu, kasar Sin za ta ci gaba da zuba makudan kudade ga kasashen waje, in ji jami'in.(Bello Wang)