in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shimfida layin dogo na SGR ta yadda ba zai gurbata muhalli ba
2017-06-08 12:08:08 cri

Ranar 31 ga watan Mayu ne aka yi bikin kaddamar da layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar Kenya wato SGR, inda aka fara aiki da shi a hukumance. An dauki shekaru 2 da rabi ne kawai aka kammala shimfida layin dogon, wato an samu ragin watanni 18 na aikin shimfida layin dogon kamar yadda aka tsara a baya. Yayin da ake shimfida layin dogon cikin sauri kamar yadda ya kamata, an yi la'akari da matakan kiyaye gurbatar muhalli.

Liu Xianfa, jakadan kasar Sin dake kasar Kenya kuma zaunannen wakilin kasar Sin a hukumar kula da harkokin kare muhalli ta MDD wato UNEP ya bayyana cewa, an tsaya tsayin daka wajen girmama matakan kare muhalli, cancantar muhalli da kiyaye muhalli yayin da ake shimfida layin dogo na SGR, ya kusa yi daidai da taken ranar muhalli ta duniya a bana wato "ba za a raba dan Adam da muhalli ba".

Kiyaye bishiyoyin Mangrove a Mombasa, wani misali ne mai kyau. Layin dogo na SGR tsakanin Mombasa da Nairobi ya ratsa wurin shan iska mai damshi na bishiyoyin Mangrove dake Mombasa. Kafin a fara aikin shimfida layin dogon, kamfanin ya gayyaci kwararru da jami'an hukumar kula da gandun daji ta wurin da su kimanta illar da aikin shimfida layin dogon zai haddasa kan muhalli, su shata layin da bai kamata a ketare ba, da kokarin rage sare bishiyoyin. Kana kuma kamfanin ya binne wasu bututun ruwa domin tabbatar da ganin ruwan teku ya shiga wurin da babu ruwan teku sakamakon shimfida layin dogon, a kokarin kiyaye bishiyoyin Mangrove. Bayan da aka kammala aikin shimfida layin dogon, bishiyoyin sun girma yadda ya kamata.

Har ila yau, masu shimfida layin dogon sun hada kai da hukumar kiyaye dabbobi ta wurin wajen kiyaye namun daji, wadanda suka kasance alamar kasar Kenya da ma wasu kasashen Afirka. Sun kuma yi nazarin nau'o'in namun daji da suke kaura da hanyoyin da suke bi a bakin layin dogon SGR, sun kuma kebe wasu hanyoyin musamman ga giwa, rakumin daji da sauran namun daji don su ketare layin dogon bisa al'adarsu da kuma yadda koguna suke gudana.

Akwai hanyoyin namun daji guda 14, gadoji guda 79 da ramukan namun daji fiye da 100 a duk bakin layin dogon da ya ratsa tsakanin Mombasa da Nairobi, wadanda dukkan namun daji har da rakumin daji ke amfani da su wajen ketare layin dogon ba tare da shinge ba.

Wani jami'in hukumar ceton giwa mai zaman kanta da ke da hedkwata a kasar Kenya dakta Bensen Okita ya ce, kila layin dogon zai kawo illa ga zaman rayuwar namun daji, amma wadannan hanyoyin musamman suna taimaka musu su yi rayuwarsu yadda ya kamata.

Ban da haka kuma, yayin da ake shimfida layin dogon na SGR, an yi shi ta yadda zai dace da muhallin wurin. An tsara fasalin tasoshin jirgin kasa a bakin layin dogon zuwa jakin daji, tsaunin Kilimanjaro, gidan mazauna wurin na fil azal, wadanda suka dace da muhallin wurin sosai.

Layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi na SGR ya samu amincewar mazauna wurin sosai saboda ingancinsa da kuma matakan kare muhalli da aka bi wajen shimfida shi. Darektan kamfanin jirgin kasa na kasar Kenya yana ganin cewa, an shimfida nagartaccen layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi na SGR ne cikin sauri, wanda ya gamsar da kowa da kowa.

Liu Xianfa, jakadan kasar Sin dake kasar Kenya kuma zaunannen wakilin kasar Sin a hukumar kula da harkokin muhalli ta MDD wato UNEP ya takaita cewa, an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi na SGR cikin hanzari kuma yadda ya kamata, musamman ma an mai da hankali sosai wajen kiyaye muhallin halittu a wurin. An yi tunanin kiyaye muhalli yayin da aka tsara aikin shimfida layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi na SGR, shimfida shi, da tafiyar da shi, wanda ya samu babban yabo daga wajen mahukunta da ma al'ummar wurin, sa'an nan ya kara taimakawa wajen yayyata shawarar "ziri daya hanya daya" a nahiyar Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China