AMISOM tace shirin horaswar ya kunshi horo na makonni biyu ga dukkan jami'an yan sanda na jahohin kudu da yammaci kasar domin koyar dasu dabarun kara inganta aikin tabbatar da tsaro, domin su bada kyakkyawar kariya ga jami'an gwamnati da sauran mutane masu muhimmanci a kasar.
Mataimakin jami'ai 'yan sandan AMISOM mai bada horon, Christopher Mumo, yace, bada horon zai taimakawa 'yan sandan Somali wajen samun kwarewa da nufin inganta sha'anin tsaron rayukan muhimman mutane a dukkan jahohin kasar baki daya.
Wannan shirin bada horon yana zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyar Al-Shababb ke bullo da sabon salo na hallaka shugabanni da manyan jami'an gwamnatin kasar.
'Yan sanda na AMISOM suna koyar da 'yan sandan kasar Somali ne da nufin sauya dabarun tabbatar da tsaro da kuma tabbatar da doka da oda a kasar.
Mumo ya ce, abu ne mai muhuimmanci su ba da kariya ga shugannin da aka zaba, bayan kammala zabukan kasar a farkon wannan shekara.(Ahmad)