in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da ECA suna makokin mutuwar babban darektan UNFPA
2017-06-08 09:39:21 cri
Kungiyar tarayyar Afirka (AU) da hukumar harkokin kudi ta kungiyar ECA a takaice suna makokin mutuwar babban darektan asusun kula da yawan al'umma na MDD Babatunde Osotimehin, kana tsohon ministan lafiyan Najeriya wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa dake birnin New York na kasar Amurka

Wata sanarwar da hukumar ta ECA ta rabawa manema labarai ta ce za ta dade tana tunawa da kyakkyawan jagorancinsa na samar da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya ga kowa da kowa, ciki har da 'yan cin samun kulawar lafiya ga kowa, musamman mata da matasa da baligai.

Hukumar ta ce a yayin da marigayin yake shugabancin asusun na UNFPA ya yi nasarar cimma wasu manyan manufofi guda uku game da matuwar mata masu juna biyu, da shirin kayyade iyali da kawar da wasu abubuwa na al'ada da ke yiwa mata da 'yan mata.

Ya kuma jagoranci kokarin asusun game da kare yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki, musamman tsakanin manyan da matasa, ta yayata amfani da kororon roba da tabbatar da cewa mata da 'yan mata sun samu magungunan kariya daga cutar HIV da harkokin da suka shafi jima'i.

Marigayi Osotimehin ya rike mukamin ministan lafiya da kuma babban darektan hukumar yaki da cutar kanjamau duk a Najeriya kafin ya kama aiki da asusun kula da yawan al'umma na MDD a shekarar 2011. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China