in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na mai da hankali kan aikin samar da isassun kayayyakin abinci
2017-06-07 11:21:16 cri

jiya Talata ne, aka yi taro ta kafar bidiyo game da aikin tabbatar da samar da isassun kayayyakin abinci na kasar Sin a nan Beijing. Bisa shirin da aka tsara, daga watan Yuni da muke ciki, kasar Sin za ta binciki matsalolin dake kawo barzana ga ayyukan samarwa da kuma adana kayayyakin abinci domin kokarin tabbatar da tsaron aikin samar da isassun kayayyakin abinci. Mr. Zhang Wufeng, shugaban hukumar kula da harkokin kayayyakin abinci ta kasar Sin ya bayyana cewa, za a kara mai da hankali kan ayyukan adana da kuma samar da kayayyakin abinci a duk fadin kasar, baya ga kara mai da hankali kan yadda ake saya, da kuma samar da kayayyakin abinci da kuma ingancinsu bisa doka ba tare da cin hanci da rashawa ba.

A halin yanzu, akwai isassun kayayyakin abinci a kasuwannin kasar Sin, kuma ana iya sayar da kayayyakin abinci kamar yadda ake so, har ma farashinsu ma bai tashi ko sauka sosai ba. Bugu da kari, ana samun kyautatuwar kayayyakin more rayuwa da suke shafar aikin sufurin kayayyakin abinci. Sannan an kara kyautata dokar dake tabbatar da ganin gwamnan kowane lardi ya dauki nauyin tabbatar da samar da isassun kayayyakin abinci. Amma yanzu tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wani sabon yanayi, wannan ya sa yanayin da kasar Sin ke ciki game da tabbatar da samar da isassun kayayyakin abinci ya fuskanci wasu sabbin matsaloli. Mr. Zhang Wufeng, shugaban hukumar kula da harkokin kayayyakin abinci ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Da farko dai, a cikin dogon lokaci mai zuwa, yanayin samar da kayayyakin abinci da kasar Sin ke ciki zai ci gaba da daidaita. Amma yanzu, yawan masara da shinkafa da ake da su ya wuce bukatar da ake da ita. Yawan kayayyakin abinci da ake ajiyewa a gidajen adana kayayyakin abinci yana da yawa. Sakamakon haka, yanzu kasar Sin tana fuskantar matsin lamba wajen saya da adana su, da kuma tabbatar da tsaro da ingancinsu a lokacin da ake adana su. Wannan ya sa, ake fuskantar wasu hadarurraka. Bugu da kari, ana noman kayayyakin abinci ne a wasu muhimman yankunan kasar. Sakamakon haka, a cikin shekaru biyu da suka gabata, yawan kayayyakin abinci da ake sufurinsu tsakanin larduna daban daban ya kai wajen ton miliyan 170. Sannan, kasuwannin cikin gida da na waje suna hadin gwiwa sosai. Yawan kayayyakin abinci da ake shigowa da su nan kasar Sin daga ketare ya kai ton miliyan dari 1 a kowace shekara. Sabo da haka, ana fatan za a kyautata aikin tabbatar da samar da kayayyakin abinci a kasuwa, musamman a lokacin da ake bukatar hakan cikin gaggawa."

A waje daya, yanzu an gano wasu matsalolin da ake fama da su a fannin tsaron sufurin kayayyakin abinci, kuma suna iya kawo cikas ga kokarin sauya salon raya masana'antun sarrafa kayayyakin abinci. Alal misali, har yanzu babu isassun dokokin da suka shafi kula da kayayyakin abinci. Mr. Zhang Wufeng ya kara da cewa, "Har yanzu ba a bullo da 'dokar kayan abinci' ba tukuna. Babu isassun dokokin da za a yi amfani da su a lokacin da ake warware batun kayayyakin abinci. Yanzu haka an shafe shekaru 10 ko fiye ana amfani da 'ka'idojin kula da ayyukan sufurin kayayyakin abinci" da "ka'idojin kula da gidajen adana kayayyakin abinci dake hannun gwamnatin tsakiyar kasar Sin". Yanzu wadannan ka'idoji ba su iya biyan bukatun da ake da su a lokacin da ake yin kwaskwarima kan aikin sufurin kayayyakin abinci da kuma yadda ake adana da amfani da su."

Game da matsalolin da ake fuskanta, hukumar kula da kayayyakin abinci ta kasar Sin ta gabatar da wasu "Shawarwari kan yadda za a karfafa tsaron kayayyakin abinci a duk fadin kasar Sin", inda aka nemi a kara mai da hankali kan ayyukan adana da kuma samar da kayayyakin abinci a duk fadin kasar, tare da kara mai da hankali kan yadda ake saya, da kuma samar da kayayyakin abinci da kuma ingancinsu bisa doka ba tare da cin hanci da rashawa ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China