in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga taron binciken sararin samaniya
2017-06-06 13:01:27 cri
A yau Talata ne, aka kaddamar da taron binciken sararin samaniya na duniya na shekarar 2017 a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga masu halartar taron.

A cewar shugaban, kasar Sin ta dora cikakken muhimmanci kan nazarin sararin samaniya, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi a fannin zirga-zirgar sararin samaniya. A sabili da haka, kasar na son hadin kai tare da sauran kasashe don bincike da kuma amfani da sararin samaniya cikin lumana, ta yadda za a tabbatar da makoma mai kyau ga daukacin dan Adam.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China