Bankin duniya ya nanata matsayin hasashensa na karuwar tattalin arzikin duniya a 2017 da kashi 2.7
A ranar Lahadi bankin duniya ya nanata hasashensa game da samun karuwar tattalin arzikin duniya da kashi 2.7 a shekarar 2017 da kuma kashi 2.9 a shekarar 2018, sakamakon samun habakar masana'antu da harkokin cinikayya.
Rahoton bankin duniyar ya bayyana cewa hasashen yiwuwar samun kyakkyawar makoma na karuwar kashi 4 bisa 100 a harkokijn kasuwancin a shekarar 2017 bayan komadar tattalin arzikin da aka samu a shekarar da ta gabata ya mayar da hasashen zuwa kashi 2.5 cikin 100.