in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soma aiki da layin dogo na SGR
2017-06-01 13:14:22 cri

A jiya Laraba 31 ga watan Mayu, an soma aiki da sabon layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar Kenya wato SGR, wanda kamfanin CRBC na kasar Sin ya gudanar da aikin sa, aikin da ya cika burin da ake da shi na samar da layin dogo ga jama'ar kasar Kenya, kana aikin ya alamta muhimmin mataki da aka kai wajen gina tsarin hanyoyin jiragen kasa na yankin gabashin Afirka da raya yankin bisa tsarin bai daya.

Da safiyar ranar 31 ga watan Mayu ne aka gudanar da kasaitaccen biki a babban filin tashar Mombasa, wadda ita ce tashar fari ga layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, don murnar soma aiki da layin dogo na SGR.

Tsawon layin dogon ya kai kilomita 472, wanda ya hade birnin Mombasa, tashar jiragen ruwa mafi girma a gabashin Afirka da birnin Nairobi, wato babban birnin kasar Kenya.

A ranar 19 ga watan Agusta na shekarar 2013, aka daddale takardar bayani kan tattara kudin aiwatar da wannan aiki a gaban shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta. A ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 2014 kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugabannin na wasu kasashe hudu, ciki har da shugaba Uhuru Kenyatta sun kalli yadda aka rattaba hannu kan yarjejeniyar tattara kudin gudanar da shi.

A ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2014, aka soma aikin gina hanyar dogo ta SGR, wanda ya lashe dalar Amurka sama da biliyan 3.8, inda kuma kashi 90 cikin dari na kudin ya fito daga rancen bankin shigi da fici na kasar Sin, kana aka yi amfani da fasahohi da ma'aunin Sin wajen gina layin dogon.

Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong ya halarci bikin, inda a madadin shugaba Xi Jinping, ya taya murnar soma aiki da layin dogo na SGR, kana shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya hau jirgin kasa na farko a kan layin. Wang Yong ya bayyana a gun bikin cewa,

"Shugaba Xi Jinping yana farin ciki game da soma aiki da layin dogo na SGR. Layin dogo na SGR nasara ce da aka samu yayin da ake aiwatar da shawarar 'ziri daya hanya daya', wadda shugaba Xi Jinping ya gabatar tare kuma da shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 da aka cimma daidaito a taron koli na Johanesburg, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, kana shi ne muhimmin aiki na raya tsarin jiragen sama, da na kasa, da hanyoyin motoci da masana'antu a tsakanin Sin da Afirka, tare da hadin gwiwar samar da kayayyaki, kuma shi ne nasarar da aka samu yayin da kasashen biyu ke sada zumunta da yin hadin gwiwa."

Wang Yong ya bayyana cewa, soma aiki da layin dogo na SGR, zai sa kaimi ga bunkasa kasar Kenya da kasashen dake yankin, da gaggauta raya masana'antu a Afirka, da aiwatar da shawarar "ziri daya hanya daya" a nahiyar Afirka da amfanawa jama'ar Afirka. Ya ce,

"Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Kenya, da rike damar soma aiki da layin dogo na SGR, don aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da amfanar jama'ar kasashen biyu ta hadin gwiwarsu, da samun moriyar juna da bunkasuwa tare."

A gun bikin soma aiki da laiyin dogo na SGR, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, yana son yin amfani da damar soma aiki da layin dogon, wajen zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Kenya. Ya ce,

"A yau, jama'ar kasar Kenya miliyan 45, tare da kasashen dake makwabtaka da mu, muna taya juna murnar wannan muhimmiyar rana tare. Ina son mika godiya ta ga memban majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong zuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da jama'ar kasar Sin bisa samar da gudummawa da goyon baya gare mu."(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China