in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar dogo ta SGR ta soma aiki
2017-05-31 13:24:30 cri

A safiyar ranar 31 ga watan Mayu, an shirya bikin soma aiki da sabon layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi ta kasar Kenya wato SGR a takaice, bikin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da manzon musamman na shugaban kasar Sin, kuma wakilin majalisar gudanarwar kasar Wang Yong za su halarta.

Kafin hakan, a ranar 30 ga watan Mayu, kamfanin CRBC na kasar Sin wanda ya gudanar da aikin gina layin dogon, da hukumar kula da harkokin layin dogo ta kasar Kenya sun cimma yarjejeniya game da gudanar da harkokin layin dogon, da kuma kiyaye shi.

Layin dogo na SGR ya hade birnin Mombasa wanda ya kasance tashar jiragen ruwa da ta fi girma a gabashin Afirka da birnin Nairobi, wato birni na zamani na kasa da kasa a Afirka. Tsawon layin dogon ya kai kilomita 472. Tun a shekarar 2013, aka amince da takardar bayani kan tattara kudin aiwatar da wannan aiki a kan idon shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta. A shekarar 2014 kuma, aka cimma yarjejeniyar tattara kudin gudanar sa kan idon firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugabannin na wasu kasashe hudu, ciki har da shugaba Uhuru Kenyatta.

A ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2014, aka soma aikin gina hanyar dogo ta SGR, wanda ya lashe dalar Amurka sama da biliyan 3.8, inda kuma kashi 90 cikin dari na kudin ya fito daga rancen bankin shige da fice na kasar Sin.

Wannan layin dogo ya kasance sabuwar hanyar jiragen kasa ta farko da aka gina bayan shekaru 100 da suka wuce a kasar ta Kenya, ta kuma zama aikin mafi girma na muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a a kasar, wadda zai yi tasiri kwarai ga tsarin layukan dogo a gabashin Afirka a nan gaba.

An gina hanyar dogon ta SGR ne bisa ma'aunin kasar Sin, kuma ta hanyar amfani da fasahohi da na'urorin kasar Sin. A yayin da ake gudanar da aikin ginin, an samar da guraban aikin yi kimanin dubu 46 ga 'yan kasar Kenya, kana an horar da ma'aikatan wurin dubu 18. A ko wane watanni uku, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai shirya taron samar da daidaito ga aikin, yayin da aikin ke jawo hankulan kasashe makwabtan sa.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, aikin gina layin dogon ya kawo karuwar GDP a kasar Kenya da karin kashi 1.5 cikin dari. Kuma idan har layin dogon ya soma aiki, za a rage kudin jigilar kayayyaki a kasar da kashi 40 cikin dari, haka kuma za a karfafa zirga-zirgar kayayyaki tsakanin kasashen dake gabashin Afirka, tare kuma da inganta cudanya, da mu'ammala, da dunkulewar yankin gabashin Afirka bai daya. A hannu guda kuma za a inganta ci gaban tattalin arzikin gabashin Afirka, da kyautattuwar zaman rayuwar jama'ar yankin.

Aikin gina layin dogo na SGR, aiki ne abun misali da zai samar alheri ga kasashen Afirka bisa shawarar "Ziri daya hanya daya". Bisa takardar da aka cimma, kamfanonin kasar Sin za su samar da hidimomin gudanar da harkoki, da kiyaye layin dogon, ciki har da rarraba ayyukan jiragen kasa, da kiyaye da gyara hanyar dogon, da jiragen kasa, kana da samar da fasahohi, da horar da kwararru na bangaren Kenya da dai sauransu. Takardar na kunshe da wa'adin aikin yarjejeniya na shekaru goma, kuma bayan shekaru biyar da fara aikin, bangaren Kenya zai tantance hidimar da kamfanonin Sin suka yi, daga baya kuma za a tsaida kuduri kan yadda za a hada kai a cikin shekaru biyar masu zuwa.

An ce, aikin tawagar kula da harkokin layin dogon na SGR wanda kamfanin CRBC na kasar Sin zai gudanar, za ta cika burin da ake da shi, na ganin ma'aikatan kasar Kenya sun iya kaiwa ga iya kula da aikin a nan gaba. Tawagar za kuma ta ba da tabbaci na horar da ma'aikatan wurin, wato ma'aikatan kasar Kenya za su karu daga kashi 76 cikin dari a shekarar 2018, zuwa kashi 80 cikin dari a shekarar 2022. Hakan kuma zai aza harsashi mai kyau ga aikin gudanar da harkokin hanyar dogon na SGR. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China