in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta fara sauya tunanin 'yan matan Chibok da aka ceto
2017-05-31 09:36:58 cri

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa ta fara cikakken shirin sauya tunanin 'yan matan Chibok da aka ceto su.

Minister harkokin mata da walwalar al'umma ta kasar A'isha Alhassan, ta ce gwamnatin kasar ta tura 'yan matan zuwa cibiyar gwajin tunanin dake babban birnin kasar Abuja, domin sake gwajin lafiyarsu, domin su samu damar cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin al'umma.

A'isha ta ce abin farin ciki ne kasancewar 'yan matan suna cikin hayyacinsu, don haka ta jaddada cewar za'a cigaba da gudanar da shirin kula da lafiyarsu da inganta tunaninsu.

Ministar ce ta karbi 'yan matan na Chibok 24 da aka fara cetowa zuwa cibiyar, yayin da su ma 'yan matan 82 da aka ceto kwanan nan suke karkashin kulawar 'yan sandan ciki na kasar, inda dukkanninsu ake cigaba da kula da lafiyarsu, za'a sada su da iyalansu bayan shirin sauyin tunanin nasu.

A ranar 6 ga watan Mayu ne aka ceto 'yan matan na Chibok su 82, bayan shafe sama da shekaru 3 a hannun mayakan Boko Haram. Suna daga cikin 'yan matan sakandaren sama da 200 da mayakan suka sace su tun a watan Afrilun shekarar 2014 a garin Chibok dake jahar Borno arewa maso gabashin Najeriyar.

A yanzu haka, dukkan 'yan matan 106 da aka ceto suna cibiyar sauya tunanin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China