in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Sin da Japan sun yi tattaunawar siyasa karo na 4
2017-05-30 12:29:43 cri

A jiya Litinin ne, Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin da Shotaro Yachi, shugaban hukumar tsaron kasar Japan suka shugabanci taron tattaunawar siyasa tsakanin manyan jami'an Sin da Japan karo na 4 a birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan.

A yayin taron, Yang Jiechi ya ce, kasar Sin ba ta sauya manufarta ta raya huldar da ke tsakaninta da Japan ba. Tana fatan cewa, Japan za ta yi amfani da lokacin da ake da shi kamar yadda ya dace, don ta tafi daidai da zamani da ma bunkasuwar kasar Sin. Za ta kuma aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma na cewa, Sin da Japan, abokai ne da ke hada kai da juna, kuma ba za su kawo wa juna barazana ba, kana kuma za ta sanya bayaninta na "bunkasuwar kasar Sin, wata dama ce gare ta" cikin manufofinta da matakanta.

A nasa bangaren kuma, Shotaro Yachi ya ce, Japan ba ta sauya matsayinta kan batutuwan Taiwan da tairhi ba. Tana himmantuwa wajen kyautata huldar da ke tsakaninta da Sin. Kana tana son hada kai da kasar Sin domin karfafa musaya a dukkan matakai, da fadada muhimman fannoni ciki har da daidaita takaddamar dake tsakanin sassan biyu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China