in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kara fadada shirin samar da makewayi mai nagarta a kasar Sin
2017-05-29 12:26:42 cri
Wani rahoto da hukumar lura da harkokin yawon bude ido ta kasar Sin CNTA ta fitar a ranar Jumma'a, ya nuna cewa tsakanin shekarar 2015 zuwa karshen watan Afrilun da ya gabata, an gina sabbi, tare da inganta wasu tsoffin ban dakuna da yawansu ya kai 52, 485 a sassa daban daban na kasar Sin.

Hakan dai na karkashin wani shiri ne da aka yi wa lakabi da "Sauyi game da makewayi" wanda aka kaddamar tun a shekarar 2015, da nufin tabbatar da nagarta, da tsaftar ban dakuna da al'ummar kasar ke amfani da su.

Shirin na shekaru 3 tuni ya kai ga kaso 92.7 bisa dari a bana. A baya dai tsarin ban dakuna da mazauna yankunan karkara ke amfani da su a kasar Sin, da ma wadanda masu yawon bude ido ke bukata ya sha fuskantar suka, wanda hakan ne ya ja hankulan mahukuntan kasar game da bukatar inganta fannin.

Bisa shirin da aka yi, Sin na fatan samar da sabbin makewayi 33,000, tare da gyara wasu 24,000 tsakanin shekarun 2015 zuwa 2017, ta yadda masu yawon bude ido za su samu damar amfani da makewayi da ya kai daraja ta 3.

Wani binciken jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan ya nuna cewa, mutane sun fara nuna gamsuwa da yanayin bandakuna a sassa daban daban na kasar Sin, inda a wannan karo kaso 80 bisa dari na masu yawan shakatawa suka nuna gamsuwarsu da tanajin da aka yi a fannin makewayi, sabanin kaso 70 bisa dari da aka samu a shekarar 2015.

Hukumar CNTA dai ta alakanta ci gaban da aka samu da sabbin kirkire kirkire tare da amfani da fasahohin zamani wajen inganta bandakunan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China