in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar WHO ta ba da izini ga wata sabuwar kungiyar likitoci ta kasar Sin
2017-05-27 13:10:43 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kungiyar likitoci masu bada agajin gaggawa ta lardin Guangdong, ta zama kungiya irinta ta biyu a kasar Sin, wadda ta samu izinin gudanar da ayyukan jin kai na gaggawa a wuraren dake da bukata a kasashe daban daban.

Hukumar WHO ta sanar da haka ne a jiya Juma'a, yayin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 70.

Kafin wannan, wata kungiyar masu aikin jinya ta birnin Shanghai na kasar Sin, ta riga ta samu makamancin wancan izinin daga hukumar.

Rahotanni na cewa, kungiyar ta lardin Guangdong, ta taba ayyukan agajin gaggawa na ceto mutane, da kuma shirya wasu manyan bukukuwa inda ta duba lafiyar mutane.

Ko a shekarar 2015, an taba tura kungiyar kasar Malaysia, inda ta halarci atisayen da ya gudana a can, tare da kammala ayyukanta lami lafiya.

A cewar hukumar WHO, kungiyoyin likitoci masu bada agajin gaggawa za su iya taka muhimmiyar rawa wajen ceton mutane tare da jinyar wadanda suka jikkata a lokacin da aka samu aukuwar bala'i.

A nata bangaren, hukumar ta na ba da izini ga wasu kungiyoyin likitoci a kai a kai, domin su gudanar da aiki a ketare. kuma ta wannan hanya, hukumar ta samu isassun kwararrun likitoci masu gudanar da aikin ceto a wuraren dake da bukata.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China