in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO za ta zama cikakkiyar mamba a kawacen kasashen duniya kan yaki da kungiyar IS
2017-05-26 11:17:33 cri
Kungiyar tsaro ta NATO, za ta zama cikakkiyar mamba a kawancen kasashen duniya kan yaki da kungiyar IS ta masu tsatsauran ra'ayi.

Sakatare Janar na kungiyar Jens Stoltenberg ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana bayan babban taron kungiyar da aka yi a jiya Alhamis.

Ya ce kasancenwar ta mamba baya nufin NATO za ta shiga gurmzu, ya na mai cewa matakin da shugabannin kungiyar mai kasashe mambobin 28 suka dauka na da zummar aikewa da sakon yaki da ta'addanci ga dnuiya.

Har ila yau, NATO za kuma ta rika shiga tattaunawa kan batutuwa da suka shafi siyasa har ma da shirya bada horo da inganta kwazon jami'ai.

Shugabannin kasashen mambobin NATO sun hadu a karon farko a sabon hedkwatar kungiyar dake birnin Brussels, inda suka tattauna kan kudin da ake kashewa kan dakaru da kuma yaki da ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China