in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na ganawa a Rwanda don tattauna zirga-zirgar jama'a a Afirka ba tare da wata matsala ba
2017-05-24 09:18:38 cri

A jiya Talata ne aka bude wani taron kwararru daga kasashen kungiyar tarayyar Afirka a birnin Kigalin kasar Rwanda, game da yadda za a saukaka zirga-zirgar jama'a tsakanin kasashen dake nahiyar Afirka.

Taron na kwanaki hudu ya hallara manyan jami'ai daga kasashe mambobin kungiyar AU, inda ake fatan za su bullo da shawarwari game da daftarin yarjejeniya da yadda za a aiwatar da shirin.

Da take karin haske game da fa'idar wannan shiri, shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin zirga-zirgar jama'a a nahiyar Afirka Katye Jackden, ta bayyana cewa, saukaka zirga-zirga tsakanin kasashen dake nahiyar ta dara batun harkokin tattalin arziki da kalubalen tsaro. Don haka ta yi kira da a aiwatar da shirin bisa mataki-mataki, duba da yadda ko wace kasa ta shiryawa lamarin.

Zirga-zirgar jama'a tsakanin kasashen dake nahiyar dai yana daga cikin shika-shikan shirin dunkulewar nahiyar waje guda. Shirin da kungiyar ta AU ta gabatar wani muhimmin mataki ne na cimma wannan buri

Ana sa ran shugabannin kasashe da gwamnatoci za su tattauna su kuma amince da wannan yarjejeniya yayin taron kolin kungiyar ta AU da za a gudanar a watan Janairun shekarar 2018. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China