in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farashin mai na ci gaba da tashi gabanin taron OPEC
2017-05-24 09:12:00 cri

Rahotanni na nuna cewa, farashin mai na ci gaba da tashin gauron zabo sau biyar a jere, yayin da kungiyar kasashen dake hako mai da ma wadanda ba sa cikin kungiyar da suka hada da kasar Rasha ke shirin ganawa a gobe Alhamis a birnin Vienna, domin duba yiwuwar kara adadin man da ya kamata a rika hakowa kan wanda aka cimma a watan Disamban da ya gabata.

Alamu na nuna cewa, za a kara yarjejeniyar, sai dai tambayar a nan ita ce har zuwa yaushe kana adadin zai haifar da karin tarisi.

A halin da ake ciki kuma, 'yan kasuwa sun zura ido kan yawan danyen man da kasar Amurka ta adana wanda hukumar ba da bayanai kan harkokin makamashi za ta bayyana a yau.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China