in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Cote d'Ivoire ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2017-05-23 13:47:02 cri

 

A jiya Litinin ne, shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar sa dake Abdjan.

A yayin ganawar tasu, shugaba Ouattara ya nuna yabo matuka game da shawarar "Ziri daya hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, inda ya nuna cewa, shawarar za ta tallafa wa kasashe masu tasowa har ma da wasu kananna da matsakaitan kasashen duniya. A saboda haka, yana fatan habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa wannan shawara da kuma tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka.

Haka zalika, ya ce, kasar Sin tana da muhimmin matsayi cikin harkokin kasa da kasa, ya kuma nuna yabo kan manufofin diflomasiyyar kasar Sin, kana ya nuna godiyar sa dangane da babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen kiyaye muradun kasar Cote d'Ivoire da ma sauran kasashen Afirka cikin shirye-shiryen kwamitin sulhu na MDD da sauran harkokin kasa da kasa. Haka kuma, yana fatan kasar Sin za ta sa gamayyar kasa da kasa da su kara mai da hankali kan yanayin da kasashen Afirka suke ciki.

A nasa bangare kuma, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana son taimakawa kasar Cote d'Ivoire wajen gaggauta raya harkokin masana'antu a kasar, domin kara karfinta na samun ci gaba da kanta. Sa'an nan, kasar Sin za ta taimaka yadda ya kamata kan ayyukan dunkulewar kasashen yammacin Afirka.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin ta na maraba da kasar Cote d'Ivoire da ma sauran kasashen Afirka da su shiga ayyukan gina "Ziri daya hanya daya", domin ta yi imani cewa, baya ga manyan shirye-shirye guda goma kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, shawarar ta "Ziri daya hanya daya" za kuma ta samar da karin damammaki ga bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China