Ministan shari'ar kasar Gambiya Aboubacarr Tambadou, ya sanar a jiya Litinin cewa, sun samu umarni daga kotun kasar da ta ba su damar haramta tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh da ya yi amfani da duk wata kadara dake nuna mallakinsa a cikin kasar.
Tambadou ya ce, umarnin kotun ya shafi wasu filaye ne da kamfanoni kimanin 131 wadanda ke dauke da sunan Jammeh, ko kuma wasu kungiyoyi masu alaka da Jammeh, ya kara da cewa, sun gano asusun ajiya na bankuna daban daban kimanin 86 masu dauke da sunan Yahya Jammeh ko kuma wasu kamfanoni dake da alama da shi kai tsaye.(Ahmad Fagam)