Tun daga ranar 15 ga wannan wata, dakarun anti-Balaka da kungiyar Popular Front for the Renaissance of Central Africa sun tada rikice-rikice a birnin Bria, wadanda suka haddasa mutane dubu 20 suka rasa gidajensu. Ya zuwa yanzu, a cikin mutane 22 da suka mutu a sakamakon rikicin, guda 17 fararen hula ne kuma saura 5 din membobin kungiyar anti-Balaka ne.
Tun daga watan Maris na bana, yanayin tsaro a kasar Afirka ta Tsakiya ya tsananta. Bisa kididdigar da kungiyar Red Cross a kasar ta yi, mutane fiye da 115 sun mutu a sakamakon rikicin da aka samu a birnin Bangassou dake kudu maso gabashin kasar. Kuma bisa kididdigar da MDD ta yi, mutane dubu 25 a cikin dukkan mazaunan birnin Bangassou dubu 35 suna bukatar taimakon jin kai. (Zainab)