UNHCR ta ce wasu karin 'yan kasar ta Somaliya na zuwa hukumar domin a tallafa musu ta yadda za su koma gida, inda ta nuna damuwa game da tsaro da rashin samun kayan agaji a Yemen.
Yemen dai ta kasance matsuguni da kuma zangon 'yan gudun hijira da bakin haure daga kahon Afirka da sauran sassan duniya. Yawancin 'yan gudun hijirar da ke kasar ta Yemen, kimanin kaso 91 ko 255,000 'yan gudun hijirar kasar ta Somaliya ne.