Wata majiyar 'yan sanda ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, daya daga cikin 'yan kunar waken yana dauke da bindiga kirar AK 47. Kuma a kalla boma-bomai biyu ne suka tashi a lokacin kai harin.
Wani ma'aikacin ceto da ke cikin wadanda ke taimakawa wadanda lamarin ya shafa, ya shaidawa manema labarai cewa, an yi wa ma'aikatan tsaron jami'ar guda hudu ciki har da masu aikin sa-kai magani, sakamakon raunin da suka ji. Koda yake babu wanda ya rasa ransa baya ga 'yan kunar waken.