in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron ATCM karo na 40
2017-05-18 20:56:53 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying ta shaidawa taron manema labarai a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta karbi bakucin taron tuntuba na yarjejeniyar Antatika (ATCM) karo na 40 da taron kwamitin kare muhalli karo na 20 wanda zai gudana daga ranar 22 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yunin wannan shekara.

Madam Hua ta kuma bayyana cewa, ana saran mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli zai halarci bikin bude tarukan tare da gabatar da jawabi.

Wannan dai shi ne karo na farko da kasar Sin za ta karbi bakuncin taron tuntubar. Yanzu haka wakilai 400 daga kasashe 42 da kungiyoyin kasa da kasa 100 ne suka nuna aniyarsu ta halartar tarukan.

Abubuwan da tarukan za su mayar da hankali akai sun hada da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar Antatika, canjin yanayi, yawon shatakawa da yadda ake ba da kariyar musamman ga Antatika da kuma yankunan gudanarwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China