Mr. Wainwright, ya ce ya damu game da yawan wadanda wannan hari ya shafa, da ma yiwuwar kara yaduwarsa, idan mutane sun koma aiki a gobe Litinin.
Wainwright ya yi kashedin cewa, sashen lafiya na kasashen da dama na iya fuskantar wannan barazana, sai dai kuma a cewar sa, dukkanin sassa ma ya dace su dauki wannan batu da muhimmanci, musamman ma wajen karfafa kariyar tsaro daga wannan sabon hari na Virus.
Kimanin sassan hukumomin lafiya 45 dake birtaniya da Scotland, ciki hadda asibitoci, da likitoci, da kwararru masu aikin fida, da ma wasu bangarorin bada hidima ta lafiya ne wannan hari ya shafa. Hakan dai ya dakatar da ayyukan likitoci da dama, baya ga nas-nas, da sauran ma'aikatan lafiya da suka rasa dama, ta amfani da muhimman bayanan mara lafiya, sakamakon wannan lamari.