in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar wakilan jama'ar Sin ya bukaci karfafa dangantaka da kasar Zambiya
2017-05-12 12:55:59 cri

A jiya Alhamis shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya tattauna da shugaban majalisar dokokin kasar Zambia Patrick Matibini.

Mr.Zhang ya ce kasar Sin tana martaba huldar dangantaka dake tsakaninta da kasar Zambiya cikin shekaru da dama da suka shude.

Ya ce kasar Sin zata yi aiki tare da kasar ta nahiyar Afrika bisa gaskiya, da kyakkyawar mu'amalar aminantaka, da sakamako na gaskiya kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar kuma za'a aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma tsakanin kasashen biyu kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma domin cin moriyar juna.

Kasar Sin tana maraba da goyon bayan da kasar Zambia ke ba ta game da batutuwan da suka shafi manufar kasar Sin game da yankunan Tibet da Xinjiang, Zhang yace, kasar Sin ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa ci gaban kasar Zambia.

Sannan ya bukaci bangaren dokoki na kasashen biyu dasu karafafa yin musayar kwarewa wajen samar da ingantattun tsare tsare da dokoki da zasu inganta yanayin kasuwanci.

Matibini ya yabawa kasar Sin game da irin tarihin da nasarori data cimma, sannan ya yaba da irin kyakkyawar dangantaka dake tsakanin kasar ta Zambiya da kasar Sin, wanda aka ginata bisa mutunta juna, daidaito da kuma cin moriya.

Ya kara da cewa majalisar dokokin Zambiya tana saran muyasar kwarewa da hadin gwiwa da majalisar tsara dokokin kasar Sin.

Matibini yana ziyarar aiki ne a kasar Sin tsakanin ranakun 6 zuwa 13 ga wannan wata bisa goron gayyatar da Zhang ya ba shi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China