in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa jami'an wanzar da zaman lafiya a CAR
2017-05-11 09:31:53 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya, kan harin da aka kai wa dakarun wanzar da lafiya na MDD dake aiki a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar jami'ai 4 tare da jikkata wasu 10.

Ana zargin kungiyar Anti-Balaka ta kasar da kai wa Dakarun na MDD da ake wa lakabi da MINUSCA hari, a ranar Litinin, a yankin Rafai-Bnagassou dake kudu maso gabashin kasar.

A cewar MDD, dakarun wanzar da zaman lafiya 'yan kasar Cambodia guda 4 ne suka mutu, inda kuma guda daga kasar Morocco ya bata.

Sanarwar da kwamitin wanda ya kunshi mambobin kasashe 15 ya fitar, ta bukaci hukumomin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya su nemo jami'in da ya bata, tare da gaggauta gudanar da bincike kan harin domin tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu ciki.

Mambobin kwamitin sun kuma jadadda cewa hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya na iya zama laifin yaki, inda suka kuma bayyana goyon bayansu ga shirin MINUSCA, don taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China