in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moon Jae-in ya ci zaben shugaban kasar Koriya ta Kudu
2017-05-10 11:04:47 cri
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar ga Moon Jae-in wanda ya lashe zaben shugaban kasar Koriya ta Kudu.

Bisa kididdigar da kwamitin zabe na kasar Koriya ta Kudu ta yi a safiyar yau10 ga wata, an tabbatar da dan takara na jam'iyyar Minjoo ta kasar Moon Jae-in ya lashe zaben shugaban kasar karo na 19, inda ya zama sabon shugaban kasar.

Moon Jae-in ya yi jawabi a filin Gwanghwamun dake birnin Seoul a daddaren ranar 9 ga wata cewa, zai rike hannun jama'a don yin kokarin raya kasa tare.

Wannan ne karo na farko da aka zabi sabon shugaban kasar Koriya ta Kudu a wani yanayi da babu shugaba a kasar a lokacin da zaben ya gudana, tun bayan da aka gyara tsarin mulkin kasar a shekarar 1987. 'Yan takara 15 ne suka yi rajista shiga zaben, biyu daga cikinsu sun janye daga shiga zaben a mataki na karshe gabannin zaben.

Bisa shirin da aka tsara, wanda ya lashe zaben shugaban kasar ya samu iko ne bayan da kwamitin zaben kasar ya tabbata a ranar 10 ga wata.

An haifi Moon Jae-in a shekarar 1953, karo na farko ya shiga takara a zaben shugaban kasar a shekarar 2012, amma Park Geun-hye ta kadashi a wancan lokacin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China