Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, bangarorin biyu sun mai da hankali wajen yin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa yaki da matsalar 'yan ci rani ba bisa doka ba, da kungiyoyi masu sa ran aikata laifuffuka da kuma yadda za a kiyaye tsaron yankin iyakar kasar da dai sauransu. Kana, Mr.Alfano ya nuna cewa, kasar Italiya za ta samar da taimako da goyon baya ga kasar Libya wajen gudanar da ayyukan dake shafar yankin iyakokin kasar da kuma kare tsaron kasar.
Sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a kasar Libya, an rufe ofishin jakadancin kasar Italiya tun daga ranar 15 ga watan Fabrairu na shekarar 2015. Sa'an nan, domin nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Libya ta fuskar sauyin mulki a kasa, an sake bude ofishin jakadanci na kasar Italiya dake kasar Libya a watan Janairu na shekarar bana, lamarin da ya nuna cewa, kasar Italiya ta kasance kasa ta farko cikin kasashen yammacin duniya wadda ta sake bude ofishin jakadancinta a kasar ta Libya. (Maryam)