in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana shirin "ziri daya da hanya daya" a matsayin na kowa da kowa
2017-05-05 20:09:55 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya furta a yau Jumma'a, a wajen wani taron manema labaru cewa, kasar Sin ce ta fara gabatar da shirin "ziri daya da hanya daya", amma shirin na bukatar bangarori daban daban su shiga a dama da su a cikin sa.

Ya ce kasar Sin ba ta da niyyar yin babakere, ko kuma toshe damar wasu, maimakon haka tana da ra'ayin "a tattauna tare, a kuma gudanar da shirin tare, gami da tabbatar da moriyar kowa".

Mr. Geng ya fadi hakan ne a matsayin martani, game da zargin da wasu kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin, cewa kasar ta gabatar da "shiri daya da hanya daya" ne don neman "shawo kan sauran kasashe". Mr. Geng ya ce ra'ayin wasu kasashen yamma kuskure ne. Duba da cewa ko da a yanzu ma, kasar Sin tana kokarin musayar ra'ayi tare da sauran kasashe, wadanda za su halarci wani taron shugabanni mai alaka da shirin na "ziri daya da hanya daya", wanda za a kira a nan birnin Beijing, tsakanin ranekun 14 zuwa ta 15 ga watan nan da muke ciki, don share fagen taron shugabanni dake tafe.

Ya ce wannan sakamako, zai kunshi ra'ayi guda na bangarori daban daban, wanda za a samu bisa gudummawar kowa, ba wai kasar Sin ita kadai ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China