in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ATI zata fadada ayyukanta a yammacin Afirka
2017-05-05 10:02:17 cri
Jami'an hukumar zuba jarin inshora ta kasashen Afrika (ATI) sun bayyana cewa kungiyar zata kara fadada ayyukanta a nahiyar Afrika.

ATI, wanda gwamnatocin kasashen Afrika 13 suka kafa ta, ta bayyana cewa zata kara fadada ayyukanta zuwa shiyyar yammacin Afrika domin baiwa kasashen kasashen da ke magana da harshen Ingilishi a yammacin Afirka damar shiga kungiyar.

Babban jami'in gudanarwa na ATI George Otieno, yace tuni kungiyar ta samu amincewar kasashen yammacin Afrika masu magana da faransanci 2 a matsayin mambobin kungiyar, amma yace suna bukatar samun mafi yawancin kasashen dake shiyyar nan da shekaru biyu masu zuwa.

ATI wanda kasashen Afrika suka kafata a shekarar 2001 domin tunkarar hadduran da za a iya cin karo dasu wajen gudanar da harkokin kasuwanci da masana'antu, kuma ya zuwa shekarar 2016 kungiyar ta samu ribar dalar Amurka miliyan 6.4.

Mambobin kungiyar ta ATI sun hada da Kenya, Uganda, Tanzania, Burundi, Malawi, Zambia, Zimbabwe, jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, Cote d'Ivoire, Habasha, Benin and Madagascar. Kuma a halin yanzu kasar Kenya ce ke sahun gaba wajen zuba jari mafi yawa.

A halin yanzu hukumar na cigaba da shawartar kasashen Ghana, Najeriya, Cameroon da kuma Saliyo domin su zama mamba a hukumar ta hanyar zuba jarin dala miliya 7.5 mafi karanci.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China