in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na matukar adawa da tsoma bakin Amurka cikin sha'anin yankin HongKong
2017-05-04 19:50:53 cri

Kasar Sin ta yi tir da zaman tattaunawa, wanda wani kwamitin koli na majalissar dokokin Amurka ya gudanar, game da sha'anin yankin Hong Kong.

A jiya Laraba ne dai kwamitin na (CECC), ya yi zaman sa na muhawara mai taken "Ko tsarin yankin Hong Kong zai dore?: da nazari game da halin da ake ciki bayan shekaru 20 da mika yankin.".

Da yake maida martani game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce sama da shekaru 20 ke nan da fara aiwatar da manufar kasa daya tsarin mulki biyu, wanda ke baiwa al'ummar HongKong damar mulkin kan su da kan su, kuma tsari ne wanda a fili ake iya ganin nasarar sa.

Mr. Geng wanda ya yi wannan tsokaci yayin taron 'yan jaridu na rana rana, ya ce Hong Kong yankin musamman ne na kasar Sin, kuma dukkanin wata harka da ta shafi yankin, ba ta shafi wata kasa ta daban ba.

Ya ce, "Muna matukar adawa da tsoma bakin ko wace kasa cikin harkokin HongKong, kuma abun bakin ciki ne yadda wasu tsiraru da yankin ke hada kai da wasu mutane daga kasashen ketare, wajen tsoma baki cikin harkokin da suka shafi kasar Sin, kuma lallai hakan ya keta ka'ida. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China