in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya sa Hamas ta fitar da sabuwar takardar siyasa yanzu?
2017-05-04 13:42:50 cri

A ranar 1 ga watan nan na Mayu ne kungiyar Hamas ta Palasdinu ta fitar da takardar ka'idoji da manufofin ta a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar, inda a bayyane, ta amince da kafa kasar Palasdinu mai 'yancin kai bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967. A ganin gamayyar kasa da kasa, hakan ya nuna cewa, Hamas ta daidaita matsayinta game da batun kafa kasar Palasdinu, sai dai a nata bangaren, Isra'ila ta mai da wannan mataki a matsayin zamba ga kasashen duniya.

Kwatankwacin tsarin dokokin Hamas da kungiyar ta Hamas ta fitar a yayin kafuwarta a karshen shekarar 1980, babu furucin da ya shafi "murkushe Isra'ila" a cikin sabuwar takardar da aka fitar, kuma takardar ta jaddada ra'ayin cewa za a fafata ne da masu ra'ayin farfado da kasar Isra'ila, a maimakon Yahudawa.

Ban da haka, sabuwar takardar ta tsaya kan cewa, filin kasar Palasdinu ya fara ne daga Bahar Rum a yamma, sa'an nan ya ratsa har zuwa kogin Jordan a gabas, wato ke nan ya kunshi kasar Isra'ila.

Manazarta suna ganin cewa, kungiyar Hamas ta fitar da wannan sabuwar takarda a daidai wannan lokaci ne, da nufin nuna yadda ake samun sulhu a tsakanin sassa daban daban na Palasdinu, don share fagen shawarwarin da shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas zai gudanar tare da takwaransa na kasar Amurka, Donald Trump.

An fara shawarwari a tsakanin Mr. Trump da Mr. Abbas a jiya Laraba. A labarin da aka bayar, an ce, tuni Trump ya tuntubi shugabannin kasashen Isra'ila da Saudiyya da Masar, da kuma Jordan, dangane da batun farfado da shawarwari a tsakanin Palasdinu da Isra'ila, kuma mai yiwuwa ne a gabatar da wani shiri game da farfado da shawarwari tsakanin sassan biyu, a yayin shawarwari tare da Abbas. Amma idan ana ci gaba da fuskantar sabani a tsakanin sassa daban daban na Palasdinu, lalle Abbas ba zai samu fifiko ba a shawarwarinsa tare da Trump.

Kafin zuwansa Washington, bi da bi ne Abbas ya kai ziyara Alkahira da Aman, inda ya gana da shugaban kasar Masar Abdul-Fattah al-Sisi, da kuma sarkin kasar Jordan Abdullah II Bin Al-Hussein. Mr. Abbas a nasa bangaren ya tsaya ga daidaita batun Palasdinu, bisa shirin kasancewar kasashe biyu, wato na kafa kasar Palasdinu dake da hedkwatarta a gabashin Kudus.

A ganin manazarta, sabbin matakan da Hamas ta dauka wani babban ci gaba ne, wanda ka iya haifar da tasiri mai kyau ga shawarwarin sulhu da za a gudanar tsakanin Palasdinu da Isra'ila.

Sai dai akwai kuma manazartan da suke ganin cewa, Hamas ta daidaita matsayinta ne, a sabili da yadda take la'akari da hakikanin yanayin da ake ciki. Ba da jimawa ba kuma, wata tawagar Fatah dake karkashin jagorancin Mahmoud Abbas ta kai ziyara zirin Gaza, inda ta yi shawarwari da Hamas, kuma sanin kowa ne Fatah ce ke rike da harkokin kudi a hannunta. Duk da cewa, kungiyar Hamas ita ce ke da iko a zirin Gaza tun shekarar 2007, amma gwamnatin Palasdinu ce ke samar da tallafin kudi ga al'ummar yankin.

Masu nazarin harkokin siyasa a zirin Gaza suna kuma ganin cewa, yadda kungiyar Hamas ta daidaita matsayinta, tare kuma da bayyana kanta a matsayin kungiyar da ke kokarin wanzar da sulhu a tsakanin al'umma, sa'an nan ta nisanta kanta daga kungiyar Muslim Brotherhood, kan yunkurin kyautata dangantaka a tsakaninta da Masar, da kuma sauran kasashen Larabawa ya zama tamkar sauyi ga manufofinta na baya.

A gun taron kaddamar da sabuwar takardar, jagoran hukumar Hamas Khaled Meshaal ya bayyana cewa, sabuwar takardar ta kasance sabon matsayin da aka dauka a sabon yanayin da ake ciki, amma ba za ta iya maye gurbin tsarin dokokin kungiyar Hamas ba, haka kuma ba ta saba da tsarin dokokin ta ba.

A game da wannan, Mohammed Shtayeh, wani kusa a kungiyar Fatah ya bayyana cewa, ya kamata a yabawa Hamas kan duk wani ci gaban da ya samu ta fannin manufar siyasa.

Sai dai kakakin firaministan kasar Isra'ila, David Keyes ya ce, a game da batun kafa kasar Palasdinu, Hamas ta ki amincewa da kasancewar kasar Isra'ila, wanda hakan tamkar zamba ce ga kasa da kasa, kuma ba za ta cimma burinta ba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China