Wani rahoto da cibiyar kwararru ta Ernst & Young's mai helkwata a birnin London ta fitar, ya nuna cewa jarin da Sin ke zubawa kai tsaye ya habaka, kana yawan guraben ayyukan yi sun karu sakamakon hakan a nahiyar Afirka a shekarar 2016 da ta gabata.
Rahoton wanda aka fitar a Larabar nan, ya nuna cewa, tun daga shekarar 2005 da ta gabata, Sin ta zuba jari a ayyuka 293 a kasashen Afirka daban daban, wadanda kimar su ta kai dalar Amurka biliyan 66.4, baya ga guraben ayyukan yi 130,750 da hakan ya samar.
Jarin da Sin ke zubawa kai tsaye a nahiyar Afirka ko FDI a takaice, ya karade sassan samar da kayayyaki da masana'antu ke bukata, da na samar da hidima, da ma fanni sarrafa kayayyaki a masana'antu.
Har wa yau rahoton ya ce irin wannan jari na dada fadada a dukkanin sassan nahiyar Afirka, kama daga kasashe masu arzikin ma'adanai kamar Afirka ta kudu, da Najeriya da kuma Angola, ya zuwa masu fidda albarkatun gona kamar Kenya. (Saminu Alhassan)