in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani babban jami'in Al-Shabaab ya mika wuya ga jami'an tsaro a Somaliya
2017-05-03 10:16:39 cri

Ministan tsaron jihar Jubaland ta kasar Somalia, Abdirashid Hassan Abdinur, ya ce wani babban jami'in kungiyar Al-Shabaab ya miki wuya ga jami'an tsaron jihar, dake garin El-wak na yankin Gedo dake kudancin kasar.

Abdirashid Abdinur ya ce, tsageran da ya mika wuya jiya, ya yi amfani ne da shirin yafiya da shugaban kasar ya gabatar.

Ministan ya ce, 'dan kungiyar ta Al-Shabaab Abdirim Sheikh Hassan wanda ya mika wuya ga jami'an tsaron jiya a garin El-Wak, shi ne jami'in dake kula da batutuwan da suka shafi lafiyar mayakan Al-Shabaab a yankin Gedo.

Wannan na zuwa ne bayan mayakan kungiyar 11 sun mika wuya ga hukumomin yankunan cikin makonni biyu da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China