in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci shugabannin yankin Galmudug na Somaliya da su warware bambancen-bambancen dake tsakaninsu
2017-05-03 09:56:14 cri

MDD da abokan hulda na kasa da kasa da ke kasar Somliya sun bukaci shugabanni a jihar Galmudug ta kasar Somaliya da su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da yin sulhu.

Wakilan MDD da kungiyar tarayyar Afirka ta AU da kungiyar tarayyar Turai da kasar Amurka, sun bayyana damuwarsu a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka rabawa manema labarai cewa, tattaunawar da aka shirya da nufin sasanta bangarorin ta ci tura.

A saboda haka, abokan huldar suka yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su guji aikata duk wani abin da zai kawo cikas ga kokarin sasantawar da ake, kana a shirye suke su shiga yunkurin sasantawar, idan har dukkan bangarorin suka amince da hakan.

Bugu da kari, abokan huldar sun bayyana gamsuwarsu dangane da matakan hawa teburin sulhu da bangarorin suka dauka a 'yan makonnin da suka gabata da nufin sasanta takaddamar dake tsakaninsu, a wani na kafa gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa, da inganta matakan tsaro da kuma raya yankin baki daya.

Tun watan Yulin shekarar 2015 ne dai Abdikarim Guled ya ke rike da mukaminsa na shugaban yankin Galmudug kafin ya yi murabus a watan Fabrairun wannan shekarar saboda dalilai na rashin lafiya.

Sai dai bayanai na nuna cewa, 'yan majalisar dokokin yankin ne suka kada masa kuri'ar yanke kauna a watan Janairun wannan shekara, saboda zargin da ake masa na rashin iya shugabanci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China