Shi dai wannan daki yana tsohon wurin da aka gudanar da bikin baje koli na duniya da aka gudanar a birnin Shanghai a shekarar 2010. Wannan shi ne dakin adana kayan tarihi kana cibiyar adana muhimman bayanai a duniya wanda hukumar kula da harkokin baje koli ta duniya dake birnin Paris (BIE) ta ayyana a hukunce domin gudanar da harkokin baje koli.
Dakin wanda gwamnatin birnin Shanghai da hukumar BIE suka gina cikin hadin gwiwa, har ila shi ne dakin adana kayan tarihi na farko a duniya da zai nuna tarihin ci gaban bikin baje koli a duniya. (Ibrahim)