in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Mongolia ta gida ya yi bikin cika shekaru 70 da zama yanki mai cin gashin kansa na farko a kasar Sin
2017-05-02 09:19:26 cri
A jiya Litinin ne aka shirya wani kasaitaccen biki a yankin Mongolia ta gida don murnar cika shekaru 70 da zama yanki mai cin gashin na farko da aka kafa a kasar Sin.

Sama da mutane 1,000 ne sanye da kayan gargajiyar yankin suka gudanar da raye-raye da kade-kaden Mongolia a dandalin birnin Ulanhot dake gabashin yankin, wurin da aka gwamnatin yankin a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1947.

Yankin Mongolia ta gida dai yana da fadin Sq kilomita miliyan 1.18, kimanin kaso 12 cikin 100 na fadin girman kasar Sin, kana yawan al'ummar yankin ya kai miliyan 4.6 kimanin kaso 1 bisa biyar na yawan shiyyar baki daya.

Bayanai na nuna cewa, cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, tattalin arzikin yankin ya karu daga Yuan miliyan 537 kwatankwacin dala miliyan 78 zuwa Yuan triliyan 1.86, kimanin dala biliyan 270, inda ya zama na daya cikin yankuna biyar na kasar masu 'yancin cin gashin kansu. Haka kuma a cikin wannan lokaci da muka ambata a sama,cinikayyar ketaren yankin shi ma ya karu daga dala biliyan 11 zuwa dala biliyan 11.7. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China