in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al-Sisi ya karrama hazikan ma'aikata yayin bikin ranar ma'aikata ta duniya a Masar
2017-05-01 12:09:04 cri
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yabawa dukkan ma'aikatan kasar kana ya bukace su da su kara kokari, cikin wata sanarwar da ya gabatarwa jama'ar kasar yayin bikin tunawa da ranar ma'aikata wanda hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasar ta shirya.

Cikin wani jawabin shugaban kasar da aka watsa ta gidan talabijin na kasar, ya bayyana wannan rana da cewa rana ce mai muhimmanci ga dukkan 'yan kasar ta Masar wadanda suka sadaukar da kansu domin gina kasar.

A lokacin bikin, al-Sisi ya karrama wasu hazikan ma'aikata 12 wadanda suka sadaukar da kansu wajen gina kasar, kana ya bada umarnin a samar da kudade kimanin miliyan 100 na kudin kasar kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5.5 domin amfani dasu a matsayin kudaden ko ta kwana na tallafawa ma'aikata.

Kasar Masar tana fama da tabarbarewar tattalin arziki tun bayan da kasar ta fada cikin tashin hankali da sukurkucewar sha'anin tsaro, lamarin da ya haifar da koma baya ga fannin yawon bude ido da kuma zuba jari daga kasashen ketare a kasar, lamarin ya talistawa gwamnatin kasar bullo da wasu dabarun farfadowa daga komadar tattalin arzikin da kasar ta fada, ciki har da wasu matakai na tsimin kudi da kuma rage kudaden tallafi da kasar ke bayarwa a fanni makamashi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China