in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron MDD kan batun nukiliyar zirin Koriya
2017-04-29 13:55:15 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya shirya taron ministoci kan batun nukiliyar zirin Koriya a jiya Jumma'a.

Da yake ba da rahoto, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce, Koriya ta arewa, ta keta kudurin kwamitin sulhu, ta yi ta neman bunkasa shirinta na mallakar makaman nukiliya, abun da ke matukar barazana ga tsaron sassan duniya da lalata kokarin da ake na kwance damarar soja a duniya da hana yaduwar makaman nukiliya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ne ya shugabanci taron a matsayinsa na shugaban kwamitin a wannan wata.

Bisa ga shirin, a yayin taron, wakilan da suka fito daga kasashe mambobin kwamitin 15 da na kasar Koriya ta kudu, za su ba da jawabi kan batun zirin Koriya da yadda ake gudanar da kudurin kwamitin sulhu kan al'amarin da dai sauransu.

Yayin ganawarsa da manema labaran kasar Sin da na ketare Gabanin taron, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, wanda shi ma ya halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa, ya ce , duk da sauye-sauyen yanayin da ake ciki, Sin na tsayawa a kan ka'idoji biyu a kan batun nukiliyar zirin Koriya, wato na farko, a tsaya kan rashin kasancewar makaman nukiliya a zirin, ko kadan kasar Sin ba ta yarda da Koriya ta arewa ta kirkiro da mallakar makaman nukiliya. Na biyu kuwa, a tsaya kan yin shawarwari wajen daidaita batun. Muddin dai shawarwari na ci gaba da gudana, za a iya tabbatar da kwanciyar hankalin zirin Koriya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China