in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar wakilin sashen Hausa a lardin Shanxi--Sabuwar fasahar zamani ta bunkasa dadadden kamfanin saka na birnin Xianyang
2017-04-29 12:13:29 cri

 

Kamfanin saka tufafi na birnin Xianyang dake lardin Shanxi arewa maso yammacin kasar Sin ya kasance wani muhimmin ginshikin bunkasa ciniki na siliki tun zamanin kaka da kakanni a kasar Sin.

Wannan kamfani ya samu shahara tun fil azal wajen sarrafa nau'o'in tufafi, koda yake kamfanin ya dan samu koma baya a harkokinsa a 'yan shekarun baya, amma a shekarar 2011, gwamnatin Sin ta sake bunkasa kamfanin inda ya dawo da aiki gadan gadan ta hanyar amfani da sabbin naurori da kuma fasahohi irin na zamani.

A halin yanzu kamfanin yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Shi dai wannan yanki na Xianyang, ya kasance daya daga cikin muhimman wuraren tarihi kasar Sin, saboda ya taba zama helkwatar mulki na daulolin Zhou, Qin, Han da kuma daular Tang wadanda keda tarihi na dubban shekaru.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China