Babban kwamandan shirin Zhang Youxia, ya bayyana cewa, shirin gwajin kawara kumbo mai ya samu nasara. Kwamitin tsakiya na JKS, da majalisar gudanarwar kasar da hukumar sojojin kasar duk sun aikewa masu bincike da ma'aikatan da abin ya shafa sakon taya murna.
Hadewar kumbon na Tianzhou-1, ya kawo karshen kashi na biyu daga cikin kashi uku game da shirin zuwa sararin samaniya na kasar Sin, kuma wannan yana daga cikin muhimmin kudurinta na kafa tashar binciken sararin samaniya nan da shekarar 2022.(Ibrahim)