Wannan birnin ya kasance daya daga cikin muhimmnan wuraren ziyara ga masu yawon bude ido daga sassa daban daban na kasar Sin da ma kasashen ketare. Wannan muhimmin waje yana da fadin murabbin mita 606, kuma an rabashi zuwa bangarori uku inda aka kawata shi tare da adana kayan tarihi da aka gano su sama da Shekaru 50 da suka gabata. Bisa ga bayanan da masana tarihi suka bayar, daulolin Zhou da Qin sun gudanar da mulki shekaru 3000 da suka gabata a wannan wuri, kuma a wancan lokacin, al'ummar zamanin sun kirkiri fasahar kere kere ta hanyar amfani da tagulla wajen kera kayayyakin bukatun yau da kullu, kamar tukwane, kwanukan cin abinci, murahun yin girke girke wukake, har ma da kayayyakin kawata muhalli da dai sauransu.(Ahmad Inuwa Fagam)