in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Rasha sun bayyana ra'ayoyinsu kan harin da Turkiya ta kai wa Iraki da Syria ta sama
2017-04-27 13:33:32 cri

Ranar 26 ga watan nan ne ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta ce, kafin kasar Turkiya ta kai harin sama kan kasashen Iraki da Syria a ranar 25 ga wata, ba ta tuntubi kawancen kasa da kasa na yaki da 'yan tawayen IS ba, lamarin da ya kawo barazana ga sojojin kawancen da ke karkashin shugabancin kasar Amurka.

A dai wannan rana, ita ma ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da labari a shafin ta na yanar gizo, inda ta ce, kafin a kammala aikin yaki da ta'addanci a Iraki da Syria, Turkiya ta kai harin sama kan dakarun Kurdawa a kasashen 2, matakin da ba zai taimaka ba wajen yaki da 'yan ta'adda, kana zai sanya al'amura su yi kamari. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China