in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin cimma nasarar kawar da gurbatar iska
2017-04-27 10:23:12 cri
Kasar Sin za ta kara kaimi wajen bincike kan hazo mai guba, a kokarin da take na yaki da gurbatar iska a Beijing da yankunan dake kewaye da ita.

Rahoton taron majalisar gudanarwa da ya gudana karkashin jagorancin Firaministan kasar Li Keqiang, ya ruwaito cewa, hukumomin gwamnati daban-daban, ciki har da hukumar kare muhalli da masana ilimi da sauran cibiyoyi ne za su yi aiki tare wajen samar da mafita.

Rahoton ya ce mai yiwuwa ne a karawa masana kimiyya dake bincike kan kawar da hazo mai guba kudade, daga kasasfin kudin kasar.

Aikin dai, zai mai da hankali ne kan abubuwan da ke jawo matsanancin gurbatar iska da takaita fitar iska mai guba da kuma kiwon lafiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China