in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta kammala karbar shawarwari don kafa sabuwar Gwamnati
2017-04-27 09:42:03 cri
Gwamnatin kasar Sudan ta ce ta kammala karbar shawarwari dake da alaka da kafa sabuwar gwamnati, kuma ana sa ran bada sanarwa a hukumance cikin mako mai zuwa.

Yayin wani taron manema labarai, Hadimin Fadar Shugaban kasar Ibrahim Mahmoud Hamid, ya ce an kammala duk wata tuntuba da ake da nasaba da kafa sabuwar gwmnatin hadin kan al'umma.

Ibrahim Hamid ya kuma alakanta jinkirin da aka samu wajen sanar da kunshin sabuwar Gwamnatin, da niyyar da ake da ita na shigar da dukkanin jam'iyyun Siyasa da kungiyoyi masu dauke da makamai da suka shiga taron neman sulhu na kasar da aka kammala a watan Oktoban bara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China