in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Ziyarar walikin sashemmu Ahmad Fagam a lardin Shanxi)Kafa yankin filin jirgin sama zai ba da gudummawa kan inganta shirin "ziri daya da hanya daya"
2017-04-26 18:28:02 cri

An kafa sabon yankin filin jirgin sama a sabon birnin Xixian na birnin Xian dake lardin Shanxi na kasar Sin ne a watan Janairun shekarar 2011. Yankin daya ne daga cikin muhimman sabbin yankuna 5 na sabon birnin Xixian na birnin Xian a lardin Shanxi Wanda ke karkashin shirin raya bunkasuwa na gwamnatin Sin.

Fadin wannan yankin na sabon Yankin filin jirgin saman ya kai murabbin kilomita 144.18, kuma alummar dake zaune a wannan yankin sunkai dubu 85, wannan yankin shine filin jirgin sama na kasa da kasa na takwas mafi girma na kasar Sin dake yankin Xianyang.

A shekarar 2016, wannan sabon filin jirgin saman ya yi jigilar fasinjoji sama da miliyan 32, kana manyan jiragen dakon kaya sun yi jigilar sama da ton dubu 234.

Sabon birnin jiragen saman zai maida hankali wajen kafa wasu muhimman kamfanoni da suka hada da wajen gyaran kananan jirage, helkwatar bunkasa tattalin arziki, wuraren yin bajekolin al'adun gargajiya, da harkokin aikin gona da dai sauransu.

Makasudun kafa wannan yankin shine manufar tabbatar da raya wasu muhimman ayyuka guda hudu na farko cikinsu shine raya harkokin kasuwanci na kasashen dake karkashin shirin ziri daya da hanya daya. Kuma ya zuwa yanzu, manyan kamfanonin kasar Sin masu yawa sun gabatar da bukatar kafa rassa a wannan sabon yanki.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China