in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Liu Yandong ta halarci bikin bude taron tattaunawa kan tunani a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu
2017-04-26 12:21:30 cri

Jiya Talata ranar 25 ga wata, aka bude taron tattaunawa kan tunani a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a birnin Pretoria, hedkwatar mulkin kasar Afirka ta Kudu. Mataimakiyar firaministan kasar Sin Madam Liu Yandong ta halarci bikin bude taron, ta kuma da ba da jawabi.

A cikin jawabin nata, Madam Liu ta bayyana cewa, tattaunawa kan tunani wani muhimmin bangare ne na cudanyar al'adu, wanda zai kara cudanyar al'adu daban daban, da yin koyi da wayar da kan juna, ta yadda za a sa kaimi wajen samun ra'ayin bai daya. Ta ce kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu su ginshikai ne na wayewar kan bil Adama, wadanda suka bayar da babbar gudummawa ga ci gaban wayewar kan bil Adam. Kuma al'ummar Sin da ta kasashen Afirka suna da hasashe kusan iri daya ta fuskar al'adu, kuma yanayin da suka taba kasancewa a tarihi, da ma yadda suke samu bunkasuwa sun yi kusan iri daya, wadanda za su ba da taimako wajen cimma ra'ayi bai daya kan tunaninsu. A cewar Madam Liu, wannan taron tattaunawa ya mayar da "raya makomar bil Adam bai daya da kuma yin cudanya da koyi daga tunanin Ubuntu na Afirka" a matsayin babban takensa. Ba kawai zai sa kaimi ga cudanyar tunani a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, da kara fahimtar juna, har ma zai taimaka wajen yin koyi da juna ta fuskar wayewar kai a tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a iya neman sabuwar hanya wajen daidaita matsalolin da duniya ke fuskanta, yayin da take kokarin samun ci gabanta.

Ban da wannan kuma Madam Liu Yandong ta nuna cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin hasashe na raya makomar bil Adam bai daya, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su yi kokarin raya makomar duniya gaba daya, ya kamata kasa da kasa su tsara ka'idojin duniya gaba daya, ya kamata kasa da kasa su gudanar da harkokin duniya gaba daya, kuma ya kamata kasa da kasa su more sakamakon bunkasuwar duniya gaba daya. Wannan hasashe ya dace da al'adun gargajiya da tunanin kasar Sin, kuma ya tsaya tsayin daka kan bin kundin tsarin MDD. A wani bangaren kuma, tunanin Ubuntu tunanin gargajiya ne na Afirka, wanda ya kasance daya daga cikin manyan ka'idojin kafuwar Jamhuriyar kasar Afirka ta Kudu.

Tunanin kuwa na jaddada muhimmancin kasancewar mutum, da zamantakewar al'umma, da ma kasa gu daya, wanda ya dace da hasashen raya makomar bil Adam bai daya, kuma zai ba da taimako wajen inganta cudanyar tunani a tsakanin Sin da Afirka, gami da aza harsashi mai inganci wajen raya makomar duniya mai haske.

Haka zakila ma Madam Liu ta yi nuni da cewa, tun can da Sin da Afirka na da kaddama bai daya. Ko da yake halin da duniya ke ciki da na halin da Sin da Afirka ke ciki suna ta samun sauyawa, amma muhimmanci da wajibcin aikin raya makomar Sin da Afirka bai daya bai canja ba. A matsayin kasa mai tasowa mafi girma da kuma nahiyar da aka fi samun yawan kasashe masu tasowa a duniya, idan Sin da Afirka na iya daidaita harkokinsu yadda ya kamata, to lamarin zai kasance gudummawa mafi muhimmanci da suka bai wa duniya da ma Bil Adam. Haka kuma Madam Liu ta furta cewa, ya kamata Sin da Afirka ta Kudu, Sin da kasashen Afirka su yi kokarin raya makomarsu bai daya yadda ya kamata, da kyautata zaman rayuwar jama'arsu, ta yadda jama'ar za su kara jin dadin zamansu.

"Ya kamata Sin da Afirka da Kudu, da Sin da kasashen Afirka su dora muhimmanci kan ra'ayoyi bai daya a tsakaninsu, da neman samun al'adunsu kusan iri daya, a kokarin raya makomarsu bai daya yadda ya kamata, bisa ka'idojin neman samun adalci, ci gaba, da ma jituwa. Ban da wannan ya kamata su taimakawa juna bisa fifikon nasu, domin sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, ta yadda jama'arsu za su kara jin dadin zamansu."

Kungiyar kula da harkokin diplomasiyyar jama'a ta kasar Sin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu su ne suka shirya wannan taron tattaunawa kan tunani a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu cikin hadin gwiwa. Taron da ya samu halartar baki fiye da 400, ciki har da ministan harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane, da jami'an gwamnatin kasar, tsoffin shugabannin kasar, wakilan sassa daban daban na al'ummar kasar, masana na kasashen biyu, da wakilan matasan kasashen biyu, da ma jakadun kasashen waje da ke kasar Afirka ta Kudu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China