in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar wakilin sashemmu Ahmad Fagam a lardin Shanxi---huldar ciniki dake tsakanin lardin Shanxi da kasa da kasa
2017-04-26 07:13:35 cri

A ranar 25 ga wannan watan mun ziyarci cibiyar bunkasa harkokin ciniki da gudanar da hulda ta kasa da kasa ta birnin Xian dake lardin Shanxi ta kasar Sin. Majalisar gudanar da mulki ta lardin Shanxi da kuma hukumar gudanarwa ta birnin Xian ne suka kafa cibiyar domin bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin birnin Xian dama lardin Shanxi baki daya. Bugu da kari wannan cibiya ta kasa da kasa an kafatane da nufin samar da sabon yanayin kasuwanci da kuma bude kofa ga kasa da kasa da nufin bude sabon babi na bunkasa tattalin arzikin kasashen dake karkashin hanyar kasuwancin siliki ta kan teku dakuma bude kofa ga kasashen dake karkakashin raya kasuwanci na ziri daya da hanya daya.

Cibiyar kasuwancin ta birnin Xian tana da fadin murabbain kilomita 120, kuma a halin yanzu, an riga an kammala gina yanki mai fadin murabbain kilomita 88 tsakanin kogin Ba da Wei.

Wannan cibiya ta kunshi harkokin sufurin hajoji ta kan tudu da ruwa harma data jiragen kasa. Wanda ya shafi ciniki na cikin gida da kasashen ketare.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China