in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun mutu sakamakon fashewar bom a wata makarantar Jamhuriyar Dagestan ta Tarayyar Rasha
2017-04-25 11:00:59 cri
Rahotanni daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Dagestan dake Tarayyar Rasha, na cewa, wani bom ya fashe a wata makarantar sakandare ta jamhuriyar a jiya Litinin 24 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dalibi daya.

An labarta cewa, bom ne ya fashe yayin da ake darasin ilmin kwamfuta. Ban da wannan, harin ya haddasa jikkatar 'yan makarantar 11, ciki hadda uku da suka galabaita.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Dagestan ta bayyana cewa, kawo yanzu dai, ana bin bahasin dalilin abkuwar harin.

Jamhuriyar Dagestan tana yankin Caucasia ta Tarayyar Rasha. Kuma dakarun haramtattun kungiyoyi kan ta da hankali a yankin, inda a kan samu tashe-tashen hankali da ayyukan ta'addanci. A kuma 'yan shekarun nan, gwamnatin Rasha ta kara karfin ta na yaki da haramtattun kungiyoyi a yankin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China