in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhammad na 5 ya zama jagoran kasar Malaysia na 15
2017-04-25 10:44:47 cri
A jiya ranar 24 ga wata ne aka gudanar da bikin rantsuwar kama aikin jagoran kasar Malaysia a fadar kasar, inda sarki Muhammad na 5 ya zama jagoran kasar na 15.

Muhammad na 5, ya yi jawabi a gun bikin, yana mai cewa, shekarar 2017 shekara ce ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kan kasar Malaysia. An kuma shaida cewa, mutane daga kabilu daban daban masu bin addinai daban, da al'adu daban, na zaune tare, da nuna girmamawa ga juna cikin lumana. Ya kuma yi fatan jama'ar kasar Malaysia za su ci gaba da hada kai da fahimtar juna, da daukar alhakin kare kasar su tare.

Don taya murnar kama aiki ga sabon jagoran kasar, kamfanin gidan waya na kasar Malaysia ya gabatar da kan sarki na musamman. Kaza lika gwamnatin kasar ta sanar da maida ranar 24 ga watan nan, a matsayin ranar hutu a dukkan kasar, kana za a gudanar da bikin nune-nune mai taken "sarkinmu" a dakin adana kayan tarihi na kasar, a ranar 2 ga watan Mayu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China